John 13

Yesu Ya Wanke Ƙafafun Almajiransa

1Ana gab da Bikin Ƙetarewa. Yesu ya san cewa lokaci ya yi da zai bar wannan duniya, yǎ koma wurin Uba. Da yake ya ƙaunaci waɗanda suke nasa a duniya, yanzu kuwa ya nuna musu cikakkiyar ƙaunarsa.

2Ana cikin cin abincin yamma, Iblis kuwa ya riga ya iza Yahuda Iskariyot, ɗan Siman yǎ bashe Yesu. 3Yesu kuwa ya san cewa, Uba ya sa dukan abubuwa a ƙarƙashin ikonsa, ya kuma san cewa daga Allah ya zo, zai kuma koma wurin Allah; 4saboda haka ya tashi daga cin abincin, ya tuɓe rigarsa ta waje, ya ɗaura tawul a ƙugunsa. 5Bayan haka, sai ya zuba ruwa a cikin kwano, saʼan nan ya fara wanke ƙafafun almajiransa, yana sharewa da tawul da ya ɗaura.

6Ya zo kan Siman Bitrus, wanda ya ce masa, “Ubangiji, kai za ka wanke ƙafafuna?”

7Yesu ya amsa, ya ce, “Yanzu ba ka fahimci abin da nake yi ba, amma nan gaba za ka gane.”

8Sai Bitrus ya ce, “Faufau, ba za ka taɓa wanke ƙafafuna ba.”

Yesu ya amsa, ya ce, “Sai na wanke ka, in ba haka ba, ba ka da rabo a gare ni.”

9Sai Siman Bitrus ya ce, “To, Ubangiji, ba ƙafafuna kaɗai ba har ma da hannuwana da kaina kuma!”

10Yesu ya amsa, ya ce, “Wanda ya riga ya yi wanka yana bukata yǎ wanke ƙafafunsa ne kawai; dukan jikinsa yana da tsabta. Ku kuwa kuna da tsabta, ko da yake ba kowannenku ba.” 11Gama ya san wanda zai bashe shi, shi ya sa ya ce, “Ba kowa ba ne yake da tsabta.”

12Da ya gama wanke ƙafafunsu, sai ya sa tufafinsa ya koma wurin zamansa. Ya tambaye su ya ce, “Kun fahimci abin da na yi muku? 13Kuna ce da ni ‘Malam,’ da kuma ‘Ubangiji,’ daidai ne kuwa, gama haka nake. 14Da yake ni da nake Ubangijinku da kuma Malaminku, na wanke ƙafafunku, haka ku ma ya kamata ku wanke ƙafafun juna. 15Na ba ku misali domin ku yi yadda na yi muku. 16Gaskiya nake gaya muku, ba bawan da ya fi maigidansa, ko ɗan saƙon da ya fi wanda ya aike shi. 17Yanzu da kuka san waɗannan abubuwa, ku masu albarka ne, in kuka yi su.

Yesu Ya Yi Maganar Bashe Shi

18“Ba dukanku nake nufi ba; na san waɗanda na zaɓa. Wannan kuwa don a cika Nassi ne da ya ce, ‘Wanda ya ci burodina tare da ni ya tasar mini.’
Zab 41.9


19“Ina faɗa muku yanzu tun kafin yǎ faru, domin in ya faru, ku gaskata cewa ni ne Shi. 20Gaskiya nake gaya muku, ‘Duk wanda ya karɓi wani da na aiko, ni ne ya karɓa ke nan. Kuma duk wanda ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne.’ ”

21Bayan ya faɗi haka, sai Yesu ya yi juyayi a ruhu, ya kuma furta cewa, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”

22Sai almajiransa suka dubi juna, suka rasa ko da wa yake. 23Sai ɗaya daga cikin almajiran, wanda Yesu yake ƙauna, yana zaune kusa da shi. 24Siman Bitrus ya taɓa wannan almajirin ya ce, “Tambaye shi, wa yake nufi.”

25Shi kuwa da yake jingine kusa da Yesu ya ce, “Ubangiji, wane ne?”

26Yesu ya amsa, ya ce, “Shi ne wanda zan ba shi gutsurin burodin nan saʼad da na tsoma cikin kwanon.” Da ya tsoma gutsurin burodin, sai ya ba wa Yahuda Iskariyot, ɗan Siman. 27Nan take bayan Yahuda ya karɓi burodin, sai Shaiɗan ya shige shi.

Sai Yesu ya ce masa, “Abin nan da kake niyyar yi, ka yi maza ka yi shi,”
28amma ba wani a wurin cin abincin da ya fahimci dalilin da ya sa Yesu ya faɗa masa haka. 29Da yake Yahuda ne maʼaji, waɗansu sun ɗauka, Yesu yana ce masa yǎ sayi abin da ake bukata don Bikin ne, ko kuwa yǎ ba wa matalauta wani abu. 30Nan da nan da Yahuda ya karɓi burodin, sai ya fita. Da dare ne kuwa.

Yesu Ya Yi Zancen Mūsun Bitrus

31Da ya tafi, sai Yesu ya ce, “Yanzu ne aka ɗaukaka Ɗan Mutum aka kuma ɗaukaka Allah a cikinsa. 32In kuwa Allah ya sami ɗaukaka a cikinsa, Allah zai ɗaukaka Ɗan a cikin kansa, zai kuma ɗaukaka shi nan take.

33“ʼYaʼyana, zan kasance da ku na ɗan ƙanƙani lokaci ne. Za ku neme ni. Kuma kamar yadda na gaya wa Yahudawa, haka nake gaya muku yanzu: Inda zan tafi, ba za ku iya zuwa ba.

34“Sabon umarni nake ba ku: Ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, ku ma ku ƙaunaci juna. 35Ta haka kowa zai san cewa ku almajiraina ne, in kuna ƙaunar juna.”

36Siman Bitrus ya tambaye shi ya ce, “Ubangiji ina za ka?”

Yesu ya amsa, ya ce, “Wurin da za ni, ba za ka iya zuwa yanzu ba, amma za ka bi ni daga baya.”

37Bitrus ya yi tambaya, ya ce, “Ubangiji, don me ba zan binka yanzu ba? Zan ba da raina saboda kai.”

38Sai Yesu ya amsa, ya ce, “Anya, za ka iya ba da ranka saboda ni? Gaskiya nake faɗa maka, kafin zakara yǎ yi cara, za ka yi mūsun sanina sau uku!

Copyright information for HauSRK